Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Zargi Kasar Australia Da Nuna Banbancin Launin Fata


Shugaban China Xi Jinping (Shi Jinping)
Shugaban China Xi Jinping (Shi Jinping)

China na kira ga ‘yan kasar cewa kar su ziyarci kasar Australia, ta na mai nuni da banbancin launin fata da kuma takalar ‘yan Asiya, a wani al’amari mai kama da yinkurin China na ganin bayan kasar ta Australia, saboda kira da ta yi cewa a gudanar da bincike kan musabbabin cutar corona.

Wata sanarwar da Ma’aikatar Al’adu da Yawon Bude Ido ta fitar ranar Jumma’a na cewa an yi ta ganin karuwar abin da ta kira, “karuwar kalamai da kuma karfi wajen nuna banbancin launin fata ga ‘yan China da Asiya a kasar Australia, saboda annobar COVID-19.”

“Ma’aikatar ta yi kira ga ‘yan China masu yawon bude ido da su farga su kauce ma zuwa Australia,” a cewar sanarwar.

A matsayin wani bangare na mai da martani, tuni kasar ta China ta kawo karshen sayen amfanin gonan Australia ta kuma maka harajin kashi 80% ga wadanda aka shigar kasar, ta na mai zargin Australia da saba ma yarjajjeniyar WTO ta wajen sayar da amfanin gonarta da matukar sauki a China.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG