Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Gargadi China Kan Mamaye Yankin Tekun Kudancin Sin


Wani jirgin ruwan yaki na kasar China
Wani jirgin ruwan yaki na kasar China

Amurka da China na yi wa junansu kallon hadarin kaji, bayan da Amurkan ta soki matakin mamaye yankin tekun kudancin Sin da China ta yi da dakaru da makamai.

Sakataren tsaron Amurka, Jim Mattis, ya soki mamaye yankin Tekun Kudancin China, da kasar ta Sin ta yi da sojoji da manyan makamai, yankin da ke dauke da tsibiran da ake takaddama akansu, yana mai cewa, matakin barazana ce da kuma nuna karfi akan kasashen da ke makwabtaka da Chinan.

Mattis ya yi wadannan kalaman ne a jiya Asabar yayin wani taron karawa juna sani da ake yi shekara-shekara kan harkokin tsaro a yankin Asiya, taron da ake wa lakabi da “tattaunawar Shangri – La,” wanda ya gudana a Singapore.

Matakin da Chinan ta dauka a yankin tekun, ya yi hannun babbar-riga da burin da muke so mu ga an cimma, hakan kuma na jefa shakku a zakutan kasashen da ke yankin, kan inda Chinan ta sa gaba.” Inji Mattis.

Sai dai a martanin da ya mayar yayin taron, wakilin China, Laftar Janar Hei Lei, ya zargi Amurka da haddasa fitina a yankin.

Ya kuma ce a matsayin China na kasa mai cin gashin kanta, tana da ikon ta girke dakaru da makamai a yankin na Kudancin Tekun Chinan, wanda a cewar shi, mataki ne da dokar kasa da kasa ta amince da shi.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG