Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Yiwuwar Za a yi Taron Koli Tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa


Shugaban Amurka Donald Trump ya tabbatar da cewa wani babban jami’in gwamnatin Koriya ta Arewa zai kai ziyara birnin New York don tattaunawa akan shirin taron koli tsakanin Trump da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un.

“Kim Young Chol, mataimakin shugaban jam’iyya mai mulki a Koriya ta Arewa zai je New York,” a cewar Trump a wani sako da ya rubuta a shafinsa na twitter.

‘Yan sa’o’in da suka gabata, rahotanni sun ce Kim Yong Chol, mataimakin shugaban jam’iyya mai mulki a Koriya ta Arewa, tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar kuma, ya tashi na tashar jiragen saman Beijing. Kafar yada labaran Koriya ta kudu, Yonhap ta ce Kim na shirin zuwa New York gobe Laraba idan Allah ya kaimu.

A makon da ya gabata ne Trump ya aikawa Kim Jong Un wasikar soke taron kolin da aka shirya yi ranar 12 ga watan Yuni, ya kuma ce tsananin fushi da kiyayya da shugaban koriya ta arewa ya nuna a wata sanarwa ce dalilin da ya sa ya dauki matakin.

Amma an cigaba da zaman shawarwari tsakanin kasashen, ciki harda ganawar da aka yi ranar Lahadi a yankin Koriya da ba ayyukan soja.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG