Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ci Gaba Da Danne Haki a Hong Kong


The White House
The White House

China na ci gaba da yakin neman wargaza dimokiradiyya da 'yancin bil adama a Hongkong, kuma masu rajin kare dimokiradiyya na ci gaba da shan wahala saboda goyon bayan 'yancin bil Adama.

A ranar 1 ga Afrilu, bakwai daga cikin manyan masu rajin kare demokradiyya a Hong Kong an same su da laifin yin taro ba tare da izini ba saboda hallartar wata zanga-zangar lumana a watan Agusta na 2019. Daga cikinsu akwai lauya mai shekaru 82, Martin Lee da fitaccen attajiri dan jarida, Jimmy Lai. Sauran masu zanga-zangar lumanar sun hada da tsohuwar ‘yar majalisar dokokin adawa Margaret Ng da kuma gogaggun masu fafutuka, Lee Cheuk-yan, Leung-Kwok, Albert Ho, da Cyd Ho.

A ranar 8 ga Afrilu, a wata shari'ar ta daban, Jimmy Lai da Lee Cheuk-yan, da kuma mai fafutuka Yeung Sam, sun amsa laifin hallartar wani jerin gwano. Lee ya ce "Na amsa laifina, amma ban yi laifi ba wajen tabbatar da 'yancin mutane cikin lumana kuma na yi imanin tarihi zai wanke ni."

Babbar zanga-zangar da aka yi a Hongkong a shekarar 2019 ta barke ne ta nuna adawa ga kudurin dokar tasa keyar wadansu ‘yan asalin Hong Kong domin shari’anta su a kotun Mainland.

A cikin watannin da suka gabata, PRC ta aiwatar da wata tsatsaurar dokar tsaro ta kasa (NSL) da sauye-sauye ga tsarin zaben Hong Kong wanda ya yi matukar rage yawan kujerun da ake zaba kai tsaye a majalisar dokokin Hong Kong.

Bugu da kari, an kame dubun dubatan masu zanga-zanga da fitattun shugabannin masu rajin kare dimokiradiyya a karkashin NSL da sauran dokoki.

Da yake magana game da hukuncin da aka yanke a ranar 1 ga Afrilu na masu rajin kare demokradiyya bakwai na Hong Kong, Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje Ned Price, ya kira tuhumar da ake yi musu da cewa “bita da kullin siyasa ne,” inda ya sake nunawa, da cewa, “matsayin da PRC da hukumomin Hong Kong ke nema don murkushe duk wani nau'i na rashin yarda da zaman lafiya a cikin gari. ”

“Amurka na ci gaba da yin Allah wadai da ci gaban da PRC ke yi wa ‘yanci da cibiyoyin dimokiradiyya a Hong Kong… Amurka na ci gaba da kasancewa tare da wadannan miliyoyin mutanen Hong Kong din da suka yi zanga-zangar lumana don kare 'yancin da ikon gashin kai da PRC ta yi musu alkawari. "

Yayin da ya ke ishara kan takunkumin da Amurka ta kakabawa jami’an China a watan Maris saboda yi wa ‘yancin dimokiradiyyan Hong Kong zagon kasa, kakakin Price ya kara da cewa,“ Za mu ci gaba da hukunta wadanan hukumomi a Beijing, wadanan hukumomi na Hongkong da ke neman wargazar da ‘yanci da ikon gashin kai wanda ya kamataHong Kong ta samu. ”

XS
SM
MD
LG