Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

CIA Ta Gano Yariman Saudiyya Na Da Hannu a Kisan Khashoggi


Yarima Mohammed bin Salman
Yarima Mohammed bin Salman

Hukumar leken asirin Amurka CIA ta gano cewa yariman Saudiyya Mohammed bin Salman shine ya bayar da umarnin a kashe dan jarida Jamal Khashoggi, a cewar jami’an Amurka.

Jiya Juma’a jaridar The Washington Post ta fara wallafa wannan labarin da hukumar CIA ta gano, inda ya yi sabani da labarin da Saudiyyar ta bayar tun farko, wanda babban mai binciken saudiiyar wanke yarima bin Salman daga kisan.

Jami’an Amurka sunce hukumar CIA ta gano cewa jami’an Saudiyya 15 ne suka yi amfani da jirgin gwamnatin Saudi zuwa Istanbul, suka kashe Kashoggi a ofishin jakadanci.

Labarin da aka wallafa na cewa hukumar leken asirin ta yi amfani da hanyoyi da dama don samo bayanai, ciki har da nadar sautin wayar talho da kanin yariman Khalid bin Salman, yayi da Khashoggi, wanda kuma shine jakadan Saudi a Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG