Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

CIA Ta Wargaza Wani Shirin Harin Kunar Bakin Wake Kan Amurka


Helkwatar hukumar leken asirin Amurka CIA.

Jami'an Amurka suka ce wani dan tsegumi ya kutsa cikin kungiyar al-Qaida a Yemen, da nufin kaddamar da harin kunar bakin wake cikin jirgin fasinja, amma sai ya mikawa hukumomin leken asiri na Saudiyya da Amurka nakiyoyin da aka shirya zaiyi amfani dasu wajen kai harin.

Hukumar leken asirin Amurka CIA a aiki kud da kud da kwayenta na ketare, ta hana wani shirin chusa wani dan harin kunar bakin wake cikin jirgin fasinja mai zuwa Amurka dauke da nakiyoyi da aka boye cikin benten maharin.

Ga abinda mai baiwa shugaban Amurka shawara kan har hana ta’addanci John Brennan yake cewa

“Muna da kwarin guiwar cewa da nakiyoyin da maharin babu guda da ya kasance barazana”.

Kwararru anan Amurka suka ce bam din kwaskawarima ne kan wadda aka shirya amfani dashi a 2009 a harin da aka so yi ranar kirsimeti da bai sami nasara ba. An tsara bam din ne ta yadda ba za a gano shi ba a bincikenda ake yi a tashoshin jiragen sama, kamar yadda Katherine Zimmerman ta cibiyar nazari da ake kira Amrican Enterprise tayi bayani:

“ Shi bam din bashi da karafa cikinsa, sabo da haka na’urorin tsaro a tashoshin jirage ba zasu iya gano shi ba. Wan nan yana lamari yana abin tada hankali ne, domin hakan yana nufin makamin yana iya wuce matakan tsaro da aka girka,har zuwa cikin jirgi.

Hukumomi suna zargin sai tayu bam din aikin wani mai suna Ibrahim Hassan Al-Asiri ne, wadda ake dangantawa da yunkurin kai hare haren bama-bamai , kuma yana da alaka da reshen al-Qaida a Yemen.

Ga abinda sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton take cewa kan wan nan sabon yunkurin: “Yunkurin harin shi kansa, ya nuna cewa ‘yan ta’addan nan suna ci gaba da kokari, suna ci gaba da kokarin samun munanan hanyoyi masu tsanani na kashe mutane da basu aikata ko wani laifi ba.”

Akwai rahotannin cewa Amurka ta kara yawan dogarawan tsaro cikin jirage dake zuwa Amurka. Sakataren tsaron Amurka Leon Panetta shima yayi tsokaci kan wan nan sabon yunkurin kawowa Amurka hari: “ Abinda wan nan lamari yake nunawa karara shine, sai kasan nan taci gaba da sa ido sosai kan mutane da suke son kawo mata hari, kuma zamu yi dukkan abinda ya zama wajibi wajen kare kasan nan.”

Tun lokacinda aka fara bore a gabas ta tsakiy a bara, mayakan sakai da suke da alaka da al-Qaida a yankin Arabia, suna ci gaba da kama kasa a kudancin Yemel. Masu fashin baki sun ce hakan ya basu karin muhalli,wan nan lamari ya karfafa yi yuwar kaiwa muradun kasashen yammacin duniya hare hare.

Kodashike hare haren da aka kai a baya bayan da jiragen yaki da basu da matuka a Yemen , ya kashe wasu shugabnnin kungiyar, hakan bai hana al-Qaida karfin kitsa kaiwa Amurka hare hare ba,yanzun ma ga sharhin Katherine Zimmerman:

“Kodashike mun sami nasarar kawar da manyan kusoshin kungiyar a yankin Arabia, al-Qaida ta sake dinke kanta kuma tana ci gaba da kasancewa babbar barazana ga Amurka.”

Masu fashin baki sun hakikance cewa kungiyar al-Qaida a yankin mashigin Arabia tana kafa sabbin sansanonin horasda ‘yan kungiyar a Yemen, kuma itace mafi karfi da zamewa babbar hadari ga Amurka.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG