Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cibiyar Al'adun Amurka Ta Shirya Muhawara Akan Zaben Kasar A Nijar


Muhawara akan zaben Amurka: Daga hagu zuwa dama- Alhaji Mustapha Kadi, Medinatu Dauda da Farfasa Isufu Yahaya

Cibiyar Raya Al'adun Amurka dake Ofishin Jakadancin Amurka a Nijar ta shirya wata muhawara domin karawa 'yan Nijar din masaniya akan yadda Amurka ke tsara zabuka da yadda ake gudanar dasu.

Wadanda suka bada kasida a wurin muhawarar sun hada da masanin kimiyar siyasa Farfasa Isufu Yahaya da 'yan rajin kare dimokradiya Alhaji Mustapha Khadi da Abdou Alhaji Idi da kuma jagorar kungiyoyin matasa Aminatu Dauda.

Kowane daga cikin wadanda suka bada kasidar ganau ne a game da harkokin zaben Amurka a sakamakon ziyarar da suka gudanar a kasar ta Amurka.

Taken muhawarar shi ne mahimmancin zabe a tafarkin dimokradiya. Wadanda suka bada kasidu sun ce tafiya da tafarkin dimokradiya aiki ne da doka da gaskiya. Idan ana son a yi aiki da dimokradiya to babu wani nuna banbanci ko na kabilanci ko na addini.

Kasar Amurka tana daraja dan kasarta ana kuma wayar da kawunan 'yan kasa akan tafarkin dimokradiya. Ba'a son zabe da kurakurai. Amurkawa sun dauki matakai nagari a fuskar dokoki da dai sauransu.

Saboda ana bin tsari bisa gaskiya da an kammala zabe duk wanda ya ci kowa zai amince da sakamakon. Babu wata jayayya ko gaddama. Amma a Afirka ba haka lamarin yake ba saboda ba zabe ake yi ba kwace ne.

A Jamhuriyar Nijar manya da matasa na bin digdigin tsarin zaben wata mai zuwa a Amurka.

Wani dalibi a Jami'ar Yamai yace a Amurka mutane na zabe ne ba tare da an sayesu ba. Suna duba cancantar dan takara ne, wanda zai fi yiwa kasar aiki. Yace abun da yakamata a dinga yi a Afirka ke nan, a dinga duba cancanta.

Wani dan kasar Kamaru dake aiki a ofishin jakadancin Amurka a Nijar yace amincewa da wata tangardar da aka gano a tsare-tsaren zabe ko a yayin gudanar dashi domin gyara a gaba shi ne abun da ya banbanta tsarin Amurka da na sauran kasashe. Misali, zaben Barack Obama wanda ya kasance bakar fata na farko abun cigaba ne. Gashi kuma a wannan shekarar an samu mace 'yar takara.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG