Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cigaba Da Tsare Zak-Zaky: 'Yan Shi'a Sun Yi Zanga-zanga


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

A cigaba da zanga-zangar nemar a sako jagoransu da 'yan Shi'a ke yi, jiya a Abuja sun ce yanzu komai fa na iya faruwa saboda tura ta kai bango; amma su ba tashin hankali su ke sha'awa ba.

Jiya ‘yan Shi’a daga jahohi daban-daban na Najeriya sun gudanar da zanga-zanga a Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja, ta bukatar a sako jagoran ‘yan Shi’a a Najeriya, Sheikh Ibrahim Yakub Zak-zaky, wanda hukumomi su ka tsare shit un bayan wani hargitsi, wanda ya biyo bayan wasu tashe-tashen hankulan da su ka yi sanadin mace-mace ciki har da ‘ya’yan Zak-Zaky din wajen shida, baya ga wasu ‘yan Shi’a da jama’ar gari da aka kashe.

Bayan zanga-zangar, wani jigo a kungiyar ta ‘yan Shi’a mai suna Abdullahi Zango, ya ce, “Yanzu a shirye mu ke mu dauki kowani irin mataki don ganin an sako ma na jagoranmu; abin fa ya isa haka; tura ta kai nago; ba wai ba mu san inda za mu samo makamai ba ne; mun san hanyoyin kasuwar bayan fage da za mu iya bi mu samo makamai, amma wannan ba ita ce manufar mu ba, don mu ba ‘yan Boko Haram ba ne. To amma a sani cewa tura fa ta kai bango.”

‘Yan Shi’ar dai da su ka zo daga jahohi dabam-dabam, sun yi ta daga kwalaye da dama masu dauke da sakonnin bukatar a sako ma su Shugabansu. Ali Babba na daya daga cikin masu zanga-zangar, kuma ya bayyana abin da ya faru da Shiekh Zak-zaky a matsayin zalunci mafi muni da aka taba yi a Najeriya, ganin yadda aka hallaka masa ‘ya’ya da mabiya.

Ga wakilinmu Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:10 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG