Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ciki Da Gaskiya: Shekaru 21 Da Kashe Wani Matashi Har Yanzu Gawarsa Na Asibitin Murtala, Satumba 14, 2020


Sarfilu Hashiim Gumel
Sarfilu Hashiim Gumel

Tun shekarar 1999 wani DPO na ‘yan sanda mai suna Solomon Enyabo, wanda afi da kwanta-kwanta a wancan lokacin ya yiwa matashi mai suna Auwalu Sha’aibu dukan da ya zama ajalinsa a jihar Kano.

Tun daga nan mahaifin wannan matashi ke tashi fadin ganin anyiwa ‘dansa Auwalu adalci, lamarin dai ya kai ga gwamnatin jiha har zuwa tarayya, daga karshe aka fara sauraron shari’a a kotu.

Duk kuwa wannan magana da ake yi gawar Auwalu ta na ajiye a Asibitin Murtala na Kano, lamarin da ya kai ga cewa sai kotu ta bayar da umarni za a iya bayar da gawar Auwalu domin a kaishi makwancinsa.

Saurari shirin Ciki Da Gaskiya.

Ciki Da Gaskiya: Shekaru 21 Da Kashe Wani Matashi Har Yanzu Gawarsa Na Asibitin Murtala, Satumba 14, 2020
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:39 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG