Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cikin Kwanaki 100 da Mulkin Amurka Ta Zama Ta Farko A Duk Fannonin Duniya-Trump


Sabon shugaban Amurka Donald Trump mai jiran gado

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump yace aikin farko da zai fara kamallawa a cikin kwannaki 100 na farkon kama mulkinsa shine aiki guda tak – “saka Amurka ta zama farko” akan duk wani al’amari a duniyar nan.

A cikin wani sakon da ya saka a dandalin duniyar gizo na YouTube, Trump yace ya umurci mukarabbansa masu shirye-shiryen kama ragamarsa ta mulki, da su lissafa mishi abubuwan da zai yi a ranar farko ta kama aikin nashi.

Yace duk wadannan aiyukkan dole su kasance manufar su itace “maido da dokokinmu da kuma aiyukkan yi ga jama’armu.”

Trump yace daya daga cikin matakan farko da zai zartas a ranar farko da kama aikin nashi shine fitar da Amurka daga cikin Kungiyar Bunkasa Harakokin Kasuwanci da Hadin Kai ta Trans-Pacific, da kuma neman a sake shata ka’idojin dake cikin yarjejeniyar kafa ta.

XS
SM
MD
LG