Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cikin Watanni Shida Sojojin Gwamnatin Sudan ta Kudu Sun Kashe Fararen Hula 114


Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da sabon hafsan sojojin kasar
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da sabon hafsan sojojin kasar

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya, MDD, yace dakarun da ke goyon bayan gwamnatin Sudan ta Kudu sun kashe akalla fararen hula 114 a tsakanin Watan Yuli na shekarar 2016 zuwa Watan Janairu na shekarar 2017 a garin Yei.

A yau jumma’a aka bayyana wannan rahoton da bangaren kula da hakkin dan adam na ofishin MDD a Sudan ta Kudu da kuma ofishin Kula da Hakkokin Dan Adam wallafa. Rahoton ya kuma bayyana “wasu ayyukan laifi na yin harbin kan mai uwa da wabi a kan fararen hula; da zaben wasu ana kashe su; Sace sace da kona kadarorin fararen hula gami da fyade wa mata, manya da kanana; ciki har da wadanda suke kokarin guduwa daga yakin.”

MDD tace Laifukan “Zasu iya zama laifukan yaki ko kuma laifukan cin zarafin bil adama” wanda ya bada damar ci gaba da bincike.

Rahoton yace fadan ya barke ne yayin da Sojojin dake goyon gwamnati suka bi abokin hamayyar Salva Kiir kuma tsohon mataimakin sa Riek Machar, “Fadan ya barke a hanyar sa ta guduwa,” Abinda takardun suka ce Kenan.

Rahoton ya ce rikicin a Yei ya kara nuna irin matsayin da akakai na dauke kai a Sudan ta Kudu, wanda ya haifar da maimaita tashe tashen hankula a fadin kasar.”

Sudan ta Kudu na cikin shekara ta hudu a cikin tashin hankali tun da fadan ya barke tsakanin magoya baya da kuma abokan hamayyar Kiir a watan Disambar 2013. MDD tace fiye da mutane Miliyan 1.8 ne a Sudan ta Kudu suka tsere daga kasar, da kuma wasu Miliyan 1.9 da suka rasa mazaunnan su sakamakon fadan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG