Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cin Hanci Da Rashawa Na Yakar Masu Yaki Da Cin Hancin Da Rashawar A Najeriya


Shugaba Mohammadu Buhari da Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry

A ganawar da Shugaba Mohammadu Buhari yayi da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya tabbatar da cewa rashawa da cin hanci ya dawo yana yakar masu yaki da cin hanci da rashawar a Najeriya.

A taron da aka gudanarwa a birnin Marrakech na kasar Morocco, inda aka tattaunawane kan matakan da za a dauka domin magance dumamar yanayi dake neman dagule lamura a duniya baki daya.

A ganawar Sakatare John Kerry, ya baiwa shugaba Buhari tabbacin cewa ko bayan shugaba Obama ya sauka daga kan mulki kasar Amurka zata ci gaba da mu’amula da cika alkawuran da tayiwa Najeriya. haka kuma Kerry yace a matsayinsa na mutum ko da baya daga cikin gwamnati zai ci gaba da yin mu’amula ta musamman da Najeriya domin bata goyon baya kan manufofi masu kyau da shugaba Buhari ya dorawa domin dawowa da kwarjini da martabar Najeriya.

Tun farko shugaba Buhari ya bayyanawa John Kerry irin matakai da nasarorin da gwamnatinsa ke ci gaba da samu wajen yaki da ta’addanci da kuma sake tsugunnar da ‘yan gudun hijira sama da Miliyan 2 wanda Najeriya ke fama da su kuma kasashen duniya ke bayar da gudunmawa.

Shugaba Buhari ya bayar da tabbacin cewa matsalar da Najeriya ke fuskanta a yanzu itace rashawa da cin hanci ya dawo yana yakar masu yaki da cin hanci da rashawar a Najeriya, wanda yake fatan kasashen duniya zasu ci gaba da baiwa Najeriya goyon bayan da take bukata.

Tuni dai shugaba Buhari ya koma Najeriya domin ci gaba da gudanar da aikin mulkin kasa bayan kammala taron lura da dumamar yanayi da aka yi a birnin Marrakech na kasar Morocco, wanda ya samu halartar kasashen duniya da shugabanni daban daban.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG