Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cin Tarar Fara Ministan Ingila Kan Karya Doka Ta Janyo Cece-Kuce a Kafofin Sadarwa


Fara Ministan Birtaniya Rishi Sunak, lokacin da ake cikin mota ba tare da ya daura bel ba.
Fara Ministan Birtaniya Rishi Sunak, lokacin da ake cikin mota ba tare da ya daura bel ba.

Ana ci gaba da cece kuce a yanar gizo game da amincewar biyan tarar da jami’an yan sandan garin Lancashire suka kakabawa Fira Ministan Birtaniya, bayan da asirinsa ya tonu a hoton kafar sadarwa na Instagram.

Faruwar wannan al’amari ya janyo ra’ayoyi mabanbanta da cece-kuje a kafofin sada zumunta na zamani, duba da girman mukami da kuma ta hanyar da aka gano ya aikata laifin.

Tun farko dai anci tarar firaministan kasar Britaniya saboda rashin daura bel a lokacin da ya dauki wani hoton bidiyo da ya kafe a kafofin sada zumunta a bayan wata mota a arewa maso yammacin Ingila.

Lokacin da Rishi Sunak ya kafe hoton bidiyon a kafar Instagram, an lura da kuskurensa a ko'ina. Wasu daga cikin wadanda suka kalli bidiyon sun mika kukansu da 'yan sandan garin Lancashire.

'Yan sandan Lancashire sun sanar ranar Juma'a, "Bayan duba wannan batu, a yau mun ba da wani mutum mai shekaru 42 daga Landan tare da tayin kayyade hukunci."

Wani mai magana da yawun Sunak ya ce Fira Minista ya nemi afuwa kan " kuskuren da ya yi" kuma ya bukaci kowa ya sanya bel.

Wannan ba shine karo na farko da fira ministan ya fara ganawa da dokar ba. A cikin 2020, lokacin da yake Ministan Kudi, Sunak, tare da Firayim Minista na lokacin Boris Johnson, an ci tarar su saboda karya ka'idojin kulle na coronavirus.

Rashin daura bel din kujerar mota a Biritaniya yana sa aci tarar dalar Amurka 620.

XS
SM
MD
LG