Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cin Zarafin ‘Yan Luwadi Na Yawaita A Faransa


Virus Outbreak France

Hare-hare kan ‘yan luwadi da madugo da kuma yawan cin mutuncinsu na dada karuwa a kasar Faransa, inda ya cilla da kashi 36% bara, bisa ga alkaluman da Ma’aikatar Cikin Gida ta fitar jiya Asabar, wanda don haka ma gwamnati ta fito karara ta ce za fa ta dakile ayyukan tsanar ‘yan luwadi a kasar.

Wannan cillawar da adadin ya yi na zuwa ne bayan da kungiyoyi mafiya tsana da kuma kai hare-hare kan ‘yan luwadi da madugo su ka bayyana shekarar 2018 da “bakar shekara.”

Participants take part in the annual Gay Pride parade in Paris, France June 24, 2017.
Participants take part in the annual Gay Pride parade in Paris, France June 24, 2017.

(Wani gangamin 'yan luwadi da madugo a birnin Paris na kasar Faransa)

Wannan sabon adadin, wanda ke nuna yadda wannan aika-aikar ta yi ta karuwa sannu a hankali, na zuwa ne a daidai jajeberin ranar Yin Tir Da Matakan Tsanar ‘Yan Luwadi da Masu Canza Halittarsu, da kuma shekaru 30 bayan Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) ta janye luwadi daga jerin halayyan da aka ayyana a zaman tabun hankali.

Bara, ‘yan sanda sun ga mutane wajen 1,870 da makiya ‘yan luwadi su ka far masu sabanin 1,380 da su ka gani a 2018, wanda ke nufin karuwar kashi 36% a yawan ‘yan luwadin da aka abin ya rutsa da su,” a cewar takardar bayanin na Ma’aikatar ta Cikin Gidan Faransa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG