Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cinikayyar Duniya: China Ta Mayarwa Da Amurka Martani


Kayan da aka shigo Dasu China Daga Amurka
Kayan da aka shigo Dasu China Daga Amurka

China ta mayarwa da Amurka martani ta fuskar cinikayya, bayan da ta kara haraji kan wasu kayayyakin Amurka da ake shiga da su cikin Chinan, wanda hakan martani ne ga makamancin wannan mataki da ita ma Amurka ta dauka a baya.

Kasar China ta kara haraji kan kayan da ake shigo da su daga Amurka da kaso 25 cikin dari, wadanda suka hada da kayan marmari, naman alade da sauransu inda kudin kayan ya kai dalar Amurka biliyan uku.

Karin harajin zai fara aiki ne nan take, a yau Litinin, kamar yadda Ma’aikatar kudaden China ta bayyana a jiya Lahadi.

China ta ce ta mayar da martani ne kan karin harajin da Amurka ta sa wa China a ranar 23 ga watan Maris din da ya gabata akan kayayyakin karafa da dalma da suke shigar da su cikinta.

Haka kuma a wani bayani da ma’aikatar cinikayyar China ta fitar a safiyar yau Litinin, ta fada cewa za ta dakatar da abin da kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO ta wajabta akanta, na rage haraji kan kayan da suke shigowa daga Amurka guda 120, ciki har da kayan marmari da sinadarin ethanol.

Ta ce harajin shigo da wadannan kayan zai karu da kashi 15 cikin 100.

Karin harajin mai da martanin na zuwa ne a lokacin da rikicin kasuwanci tsakanin Amurka da China yake kara kamari.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG