Accessibility links

Kananan yara tsakanin wata shida zuwa shekaru uku sukan yi fama da wani irin ciwon kunne da ake kira Otitis media, wanda yake ciwo a tsakiyar kunne.

Kananan yara tsakanin wata shida zuwa shekaru uku sukan yi fama da wani irin ciwon kunne da ake kira Otitis media, wanda yake ciwo a tsakiyar kunne. Ciwon kunnen yafi faruwa da damina kuma yana zuwa da zazzabi wani lokaci mai tsanani, sai dai sau da dama bai cika zama wani abun damuwa ba.

Akwai kuma wani ciwon kunnen da ake kiransa otitis external, wanda shi kuma yake shafar wajen kunne. Koda yake yara basu cika kamuwa da shi kamar na farkon ba. Yawanci kananan yara suna fama da ciwon tsakiyar kunne, musamman kananan yara daga cikin wannan jerin:
• Yaran da aka Haifa basu kai lokacin haihuwa ba
• Yara da suke yawan jin sanyi sosai
• Yara wadanda basa son wari, kamar hayakin taba da sauransu
• Yaran da ba’a basu nono ba
• Yaran da aka baiwa abincin gwangwani

Dalilai
Wasu kwayoyin cuta suke kawo ciwon tsakiyar kunne. Kwayoyin cutar na tafiya daga bayan makogoro yayinda Eustachian tube ta lalace, wannan ke kawo ciwon tsakiyar kunne. Shi yasa yara masu yawan jin sanyi ko masu fama da ciwon makogoro ke kamuwa da ciwon kunne. Otitis external shi kuma yawanci yana faruwa saboda rashin tsabtar fatar jiki da kwayar bacteria.
Alamun ciwon:
Ciwon cikin kunne (Otitis media), yawancin manyan yara suna fama da kaikayin kunne da yawan zafi. Kananan yara basa iya Magana, amma zasu kasance da zazzabi marar misali. Hakanan zasu kasa yin barci, su rika sosa kunnensu har yayi jinni, kuma suna kasa iya sauraron kara ko amo. Za’a iya samun fitar ruwa mai kwayoyin cuta daga kunnuwan.

Ciwon bayan kunne shima yana da zafi sosai, yana sa kuraje a bayan kunnuwa.

Magani:
• Ana iya ba yara kasan wata shida maganin kashe kwayoyin cuta (Antibiotics)
• Shan maganin rage zafin ciwon
• Yara suna jin sauki yayinda suka fara amfani da maganin kashe kwayoyin cuta. A nan yana da muhimmanci ga Iyaye su kiayye umurnin likita har karshe
• Shan Topical antibiotics da man shafawa suna maganin otitis external
Sake ganin likita na da amfani idan yaron yana da ciwon kunne ko yana amai sosai; idan kuma yana da zazzabi fiye da sa’a 48, da kumburi bayan kunne, idan yana barci sosai, kuraje a kunne, baya ji sosai ko gaba daya.

Kariya
• Wanke hannuwanka da na yaro
• Shayar da yara da nonon uwa
• Dena ba yara abincin kwalba lokacin suna kwance
• Dena amfani da kayan susa
• Dena shan taba a dakin da kananan yara suke
• Yiwa yaro rigakafi da yana rage wannan ciwon
• Yin allurar rigakafin mura mai zafi (Flu vaccine) kowacce shekara
A karshe, idan yaro ya kamu da ciwon kunne:
• Kada ayi amfani da auduga a kunnen, domin zata iya kara girman kwayar cutar
• Kada a diga maganin kashe kwayoyin cuta a kunnuwan yara, zai iya kawo fashewar kunne
• Kada a share kunne da auduga domin kauda danko kunne.
XS
SM
MD
LG