Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

 Corona: Duniya Ta Kau Da Kai Daga Batun Hadarin Bahar Rum


Wasu bakin haure cikin tsaka mai wuya a Bahar Rum

Bakin haure na ta ketara tekun Bahar Rum, amma kuma kasashen Turai sai dada rufe tasoshin jirgin ruwansu su ke yi, gashi kuma babu wani jirgin ruwa na ayyukan jinkai da ke gudanar da ayyukan ceto. Yayin da labaran da su ka shafi cutar coronavirus ke mamaye kafafen yada labarai, ‘yan raji na fargabar cewa tekun Habar Rum zai zama wani fagen mummunan bala’i wanda aka kau da kai daga gare shi.

Cikin ‘yan makonnin nan wasu bakin haure kalilan sun sauka wasu gabobin ruwan Turai, ciki har da wasu 79 wadanda a makon jiya su ka isa Italiya, kasar da tun kafin bullar cutar coronavirus ta fuskanci suka saboda kin yadda jiragen ruwa masu dauke da ‘yan gudun hijira su shiga tashoshin jiragenta.

Kungiyoyin kasa da kasa da kuma kungiyoyi masu zaman kansu na cewa lamarin da ban tsaro, ganin yadda tun a makon jiya aka tsai da duk wasu ayyukan ceto a tekun na Bahar Rum.

EU Libya Migrants
EU Libya Migrants

(Wani aikin ceton wasu bakin haure a Bahar Rum)

“Muddun babu taimako a teku kuma kasashe su ka shiga jan kafa kan batun ayyukan ceto da kuma barin mutane su sauka, wata ran sai mun ga wata mummunar matsala ta jinkai,” a cewar Vincent Cochetel, manzon musamman na yankin tsakiyar Meditareniya tare da Babban Kwamishinan Majalisar Dinkin Duniya kan Harkokin ‘Yan Gudun Hijira (UNHCR).

Ya kiyasta cewa cewa mutane 179 sun mutu a tekun tun daga watan Janairun wannan shekarar.

Kasashen Italiya da Malta sun rufe tasoshin jiragen ruwansu a farkon watan Afirilu a yayin da annobar corona ke addabar nahiyar Turai sosai. Wani zubin ma, jiragen ayyukan ceto biyu ne kadai su ka yi ta aika - - wato da Alan Kurdi wanda wata kungiyar da ke Jamus mai suna Sea-Eye da kuma Aita Mari wadda wata kungiyar kasar Spain mai suna Maydayterraneo ke gudanar da su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG