Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Coronavirus: Adadin Najeriya Ya Kusa 500


Wani yanki a Wuhan da ke China inda cutar coronavirus ta fara bulla
Wani yanki a Wuhan da ke China inda cutar coronavirus ta fara bulla

Bayan da aka samu karin mutum 51 da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya, adadin wadanda cutar ta harba ya kai 493.

Hukumar kare yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya ce ta bayyana karin adadin a shafinta na Twitter a ranar Juma’a.

“Daga karfe 10:10 na dare, 17 ga watan Afrilu ana da mutum 493 da aka tabbatar suna da #COVID19 a Najeriya.” NCDC ta ce.

Hukumar ta kuma ce mutum 159 aka sallama, sannan 17 sun mutu.

Ga jihohi da aka samu karin mutum 51 kamar yadda NCDC ta wallafa a shafinta.

Legas – 32

Kano – 6

Kwara – 5

Abuja – 2

Oyo – 2

Katsina – 2

Ogun – 1

Ekiti – 1

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG