Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Coronavirus: Amurka Za Ta Tallafawa Kananan 'Yan kasuwa


Yayin da shugaba Donald Trump yake karin haske kan halin da ake ciki dangane da yaki da cutar coronavirus
Yayin da masu kananan sana'o'i a Amurka ke ta fadi tashin ganin sun tsira da sana'o'insu sanadiyyar cutar coronavirus da ta sa ake ta rufe wuraren kasuwanci, gwamnatin Amurka na shirye-shiryen ganin ta tallafa masu.
Shagunan sayar da abinci da sauran masu kananan sana'o'i na ta rufe kantunansu a sassan Amurka a wani mataki na ganin an dakile yaduwar cutar coronavirus da ke bazuwa a kasar.
Ya zuwa ranar Juma'a, mutum 190 suka mutu sanadiyyar cutar a Amurka sannan wasu 16,000 ke dauke da ita.
Tuni dai hukumar da ke kula da kananan sana'o'i a Amurka ta rage kudin ruwan da ake karba daga hannun kananan 'yan kasuwa.
Hakan faruwa ne yayin da Majalisar dokokin ma take shimfida wasu tsare-tsare na tallafawa tattalin arzikin kasar.
Kusan rabin daukacin adadin ma'aikatan Amurka na aiki ne da kananan wuraren kasuwanci, inda akan samu wasunsu da ma'aikatan da ba su fi 20 ba.
Ba kamar kananan masana'antu ba, manyan kamfanoni a Amurka na da karfin da za su iya zama da kafafunsu ko da an fuskanci komadar tattalin arziki.
Baya ga gwamnati, akwai kuma manyan kamfanoni irinsu Facebook wanda ya yi alkawarin ba da tallafin dala miliyan 100 ga kananan masana'antu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG