China da Korea ta Kudu, sun samu karin adadin mutanen da ke kamuwa da cutar Coronavirus a yau Talata, yayin da kasuwar hannayen jari a Japan ta sake girgiza a karo na biyu, kwana guda baya da kasuwannin hannayen jari a sauran sassan duniya su ma suka girgiza.
Hakan na faruwa ne yayin da Shugaba Donald Trump, ya nemi Majalisar Dokokin Amurka da ta ba shi dala biliyan biyu-da-rabi domin yakar cutar.
Jami’an kiwon lafiya a China, sun ce akwai mutum 71 da suka mutu kana an samu wasu dari-biyar-da-takwas da suka kamu da cutar, abin da ya kai adadin mace-macen zuwa sama da 2,600 kana wasu mutum sama da dubu 77 suka kamu da cutar.
Baya ga Chinar, Korea ta Kudu, ita ce kasa ta biyu da cutar ta fi shafa, inda mutum dubu daya suka kamu da ita sannan goma suka mutu.
Ita ma kasar Iran ta bayyana cewa adadin wadanda suka kamu ya kai 95, sannan 15 sun mutu.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 18, 2021
Kungiyar Kasuwanci ta Duniya Na Bukatar Sabon Salon Gudanarwa-Dr. Ngozi
-
Fabrairu 18, 2021
Guterres Ya Yi Kiran a Samar Da Tsarin Bai Daya Na Rigakafin Coronavirus
-
Fabrairu 16, 2021
Kungiyar WTO Ta Gabatar Da Sabuwar Shugaba Ngozi Okonjo-Iweala
-
Fabrairu 16, 2021
Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) Ta Aminta Da Riga Kafin AstraZeneca
Facebook Forum