Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Coronavirus: Halin Da Ake Ciki A Najeriya Na Kara Muni


Wasu kayan magungunan da China ta kai Najeriya

Cibiyar hana yaduwar cututtuka a Najeriya, NCDC, ta bayyana cewa an samu karin masu dauke da cutar Corona Virus a kasar a yayin da cutar ta bazu zuwa jihohi 27 ya zuwa yanzu.

Cibiyar ta bayyana cewa duk da aiki tukuru da hukumomin lafiya ke yi na dakile cutar, lamarin ya ci tura domin cutar na cigaba da bazuwa a kasar.

A halin yanzu an samu bullar cutar ta COVID-19 a jihohi 27 na Najeriya ciki har da Birnin Tarayya kamar yadda alkaluman Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka a kasar wato NCDC ta tabbatar.

Ministan Kiwon Lafiya Osagie Ehanire ya ce ya zuwa karfe 11.30 na daren ranar Jumma'a an samu karin mutane 114 wanda ya kawo jimlar mutane 1,095 da cutar ta harba a fadin Najeriya. An sallami mutane 208 daga asibiti sannan mutane 32 sun riga mu gidan gaskiya.

Jihohin da cutar ta bulla a karon farko a baya bayan nan sun kasance Adamawa a yankin Arewa maso Gabas da jihar Filato a yankin Arewa ta Tsakiya.

Har ila yau jihar lagos ce ke kan gaba da mutane 657 sai Birnin Tarayya Abuja da da mutane 138, Kano 73, Ogun 35,Gombe 30, Katsina 21,Osun 20,Edo 19,Oyo 18,Borno 15,Kwara 11, Akwa Ibom 11, Kaduna 10, Bauchi 8, Delta 6,Ekiti 4, Ondo 3, Ribas 3, Jigawa 2, Enugu 2, Niger 2, Abia 2, Zamfara 2, Sokoto 2, Benue 1, Anambra 1, Adamawa 1 sai Filato 1.

Wani abu da ya dauki hankali shi ne cewa an samu jami'an kiwon lafiya 40 wadanda suka kamu da cutar a fadin kasar amma Sakataren Gwamnati Boss Mustapha, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Kar ta kwana da Shugaban Kasa ya kafa, ya ce Kamfanonin Inshora na kasar sun kawo dauki, inda suka bada kudi Naira miliyan 112,500 da zai zama Inshora na ma'aikatan kiwon lafiya 5,000 da suke sadaukar da rayuwarsu kullum wajen yin ayyukan agaji na kokarin dakile cutar Corona Virus.

Ga Madina Dauda da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:30 0:00


Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG