A yau Talata, jami’an kiwon lafiya a China, sun tabbatar da cewa mutum dubu 72 ne suka kamu da cutar coronavirus ya zuwa yanzu, yayin da adadin wadanda suka mutu ya doshi 1,900.
Wadannan alkaluma na baya-bayan nan, sun hada da mutum 98 da suka mutu da kuma mutum 1,886 da cutar ta harba.
Lamarin da ya sa hukumomi suka hana shige da fice a wasu yankuna, a wani mataki na dakile yaduwar cutar.
A jiya Litinin, Babban Darektan Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce, alkaluman baya-baya nan da hukumomin China ke fitarwa, na nuna cewa ana samun raguwar masu kamuwa da cutar, amma ya ce akwai bukatar a bi abin sannu-a-hankali.
“Kamata a yi taka-tsatsan kan yadda ake bayyana alkaluma, al’amura kan iya sauyawa yayin da cutar ke kara shafar wasu yankuna, saboda haka, ya yi wuri a ayyana cewa za a ci gaba da samun raguwar alkaluman.” Inji Ghebereyesus.
Kafar talbijin din kasar ta China, ta ruwaito cewa daya daga cikin wadanda suka mutu a yau Talata har da Shugaban Asibitin Wuchang da ke yankin Wuhan, inda cutar ta fi kamari.
Za ku iya son wannan ma
-
Yuni 09, 2023
Kungiyar ISIS Na Kokarin Farfado Da Karfinta a Duniya
Facebook Forum