A wani mataki na dakile yaduwar cutar Coronavirus, rahotanni daga Najeriya na nuni da cewa, hukumomin kasar sun kara mayar da hankalinsu kan matafiyan da ke shiga kasar musamman ma daga China.
A yankin Wuhan na kasar China cutar Coronavirus ta barke inda har ta kashe mutum 82 yayin da wasu dama ke samun kulawa.
An samu bullar cutar ma a wasu kasashe kamar Amurka da kuma Ivory Coast a nahiyar Afirka.
Matakan da hukumomin Najeriyar ke dauka sun biyo bayan yadda cutar ke yaduwa zuwa sassan duniya cikin sauri.
Daga cikin matakan akwai duba lafiyar matafiya da suka shigo kasar daga kasashen da wannan lamari ya shafa.
Shugaban cibiyar yaki da cututtuka ta Najeriya Dr. Chikwe Ihekweazu, ya ce yanzu dai suna duba kayan matafiya da suka shigo Najeriya ta filayen jiragen sama, da zuba ido don gano yiwuwar wannan sabuwar kwayar cutar.
Binciken ya nuna ba tsananin fargabar cutar kamar yadda aka gani lokacin barkewar cutar Ebola da ta sanya daukar jita-jitar wanka da shan ruwan gishiri da ya sanya asarar rayuka.
A saurari rahoto cikin sauti.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 24, 2021
NAJERIYA:Abdurrasheed Bawa Ya Zama Sabon Shugaban EFCC
-
Fabrairu 24, 2021
Har Yanzu Ana Zaman Zullumi A Jihar Kebbi
-
Fabrairu 24, 2021
Rashin Adalcin Gwamnati Ke Sa Mu Yin Garkuwa Da Mutane- Shehu Ragab
-
Fabrairu 24, 2021
Hira Da Wata Da Aka Yi Garkuwa Da Ita A Jihar Naija
-
Fabrairu 24, 2021
'Yan Ta'adda Sun Yi Ma Wasu Mutane Yankar Rago A Maiduguri
Facebook Forum