Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce lokaci na kure wa a kokarin da ake yi na dakile yaduwar cutar Coronavirsu.
Wadannan kalamai na zuwa ne yayin da adadin wadanda ke kamu wa da cutar ke ci gaba da karu wa.
A jiya Juma’a, Babban Darektan hukumar, Tedros Adhanom Ghebereyesus, ya ce, duk da cewa ana matakin da za a iya dakile yaduwar cutar, “ya yi garagdin cewa,” “damar da ake da ita na ci gaba da tsukewa.”
"Damar da ake da ita wajen dakile yaduwar cutar na ci gaba da raguwa, ana matakin da za a iya datse yadywar cutar, amma yayin da muke yin hakan, ya kamata mu zauna cikin shirin ko-ta-kwana.” Ghebereyesus ya ce.
Kalaman na Gheberyesus na zuwa ne a daidai lokacin da bayanai ke nuni da cewa, cutar na kara bazuwa a Korea ta Kudu.
Hukumar yaki da yaduwar cutuka a kasar ta ambato cewa, an samu sabbin mutum 229 da suka kamu da cutar.
Wannan na nufin adadin masu dauke da cutar ya kai 433 a kasar ta Korea ta Kudu.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 18, 2021
Kungiyar Kasuwanci ta Duniya Na Bukatar Sabon Salon Gudanarwa-Dr. Ngozi
-
Fabrairu 18, 2021
Guterres Ya Yi Kiran a Samar Da Tsarin Bai Daya Na Rigakafin Coronavirus
-
Fabrairu 16, 2021
Kungiyar WTO Ta Gabatar Da Sabuwar Shugaba Ngozi Okonjo-Iweala
-
Fabrairu 16, 2021
Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) Ta Aminta Da Riga Kafin AstraZeneca