Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Coronavirus: Najeriya Na Da Mutum 214 - NCDC


Ministan Lafiya a Najeriya, Dr. Osagie Ehanire

Sa'o'i kadan bayan da hukumomi a Najeriya suka sauya alkaluman mutanen da cutar coronavirus ta kama a kasar, hukumar kare yaduwar cututtuka ta NCDC ta ce adadin ya kai 214.

Da yammacin ranar Asabar NCDC ta ce mutum 209 suka kamu da cutar ba 210 kamar yadda aka sanar a ranar Juma'a ba. https://bit.ly/2RbWfsW.

Amma sa'o'i bayan gyara wannan kuskure, hukumar ta ce adadin ya kai 214 a yau.

"Da misalin karfe 10:10 na dare ranar 4 ga watan Afrilu, mutum 214 ke dauke da cutar #COVID19 a Najeriya." Shafin NCDC na Twitter ya ce.

Adadin ya haura 209 ne bayan "an samu sabbin mutum biyar da #COVID19 a Najeria, uku a Bauchi, biyu a Abuja." NCDC ta ce.

Ya zuwa yanzu, mutum hudu sun mutu an kuma sallami 25 a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG