Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Coronavirus Ta Haddasa Durkushewar Tattalin Arzikin China


Matsalolin annobar cutar coronavirus sun durkusar da tattalin arzikin China a watanni ukun farkon wannan shekarar, lamarin da ya sa dole hukumomin kasar su tashi tsaye don farfado da tattalin arzikin a yayin da rashin ayyukan yi ke barazana ga zamantakewar al’umma.

Annobar wadda ta fara barkewa a tsakiyar lardin Hubei na kasar China a karshen shekarar da ta gabata, ta tsayar da harkoki cik a kasar ta biyu a karfin tattalin arziki a duniya, yayin da aka hana zirga zirgar jama’a da ababen hawa, da kuma rufe masana’antu da kasuwanni.

Yayin da ake dage dokokin hana zirga zirga a hankali, ana ci gaba da aiwatar da irin wannan dokar a wasu manyan birane na duniya da annobar ta yi wa illa, wanda hakan kuma zai yi mummunan tasiri akan China a bangaren fitar da kayayyaki.

Masu fashin baki na hasashen tattalin arzikin China na cikin gida ya yi kasa da kashi 6.5 cikin dari daga watan Janairu zuwa Maris a farkon shekarar nan, kamar yadda kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a ta kamfanin dillancin labaran Reuters ta nuna.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG