Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Adadin Mace-mace a Amurka Ya Doshi Dubu 100


Ana tsammanin adadin mutuwar Amurkawa daga cutar coronavirus zai kai 100,000 nan da 'yan kwanaki masu zuwa.

Wata muhimmiyar alama ita ce yadda shafin farko na Jaridar New York Times na ranar Lahadi ya wallafa sunaye da bayanan wadanda suka mutu sakamakon cutar hade da wasu bayanai da aka tattaro daga wasu kafafen yada labarai da ke nan Amurka.

Kanun labaran jaridar na jiya Lahadi cewa ya yi “adadin mace-mace a Amurka ya doshi dubu 100 – asarar da ba zai misaltu ba.”

Yawan mutanen Amurka da suka mutu a safiyar Lahadi, ya zarce 97,000, a cewar Jami’ar Johns Hopkins.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da adadin wadanda cutar ta COVID-19 ta harba a duk fadin duniya yah aura miliyan 5.3, kamar yadda jami’ar ta Johns Hopkins ta bayyana yayin da wadadin wadanda suka mutu ya suka haura dubu 342,000.

A karon farko tun da ta fara ba da rahoton samun masu kamuwa da cutar a watan Janairu, China, kasar da cutar ta fara barkewar, ba ta ba da rahoton samun sabbin wadanda suka harbu da cutar ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG