Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Adadin Mace-Mace A Italiya Ya Dan Ragu Ya Zuwa Talata


A yau Talata kasar Italiya, wadda a yanzu ta fi fuskantar munin annobar cutar coronavirus, ta bada rahoto akan yadda adadin wadanda suke mutuwa da cutar kullum, da wadanda suke kamuwa da cutar yake raguwa cikin kwanaki uku a jere.

Adadin mutum 601 da aka bada rahoton sun mutu ya zuwa jiya Litinin bai sauya ba, amma kuma gaba daya an samu dan ci gaba daga kusan mutum 800 da suka mutu a ranar Asabar da ta gabata.

Kasar Italiya ta bada sanarwar mutuwar sama da mutane 6,000 kana kuma ita ce kasa ta biyu da take da adadi mafi yawa na wadanda suka kamu da cutar.

Hukumomin kasar sun dakatar da shige da fice tsawon makonni biyu da suka gabata, a kokarin da suke yi na shawo kan yaduwar kwayar cutar da yanzu haka ta yadu zuwa kusan kowacce kasa a duniya.

Koriya ta Kudu, wadda ita ce ta ke kan gaba ta fannin inda annobar cutar tafi kamari a kasashen duniya, ta nuna irin ci gaban da take samu, inda ta bada rahoton sabbin kamuwa da cutar mutuum 76 a yau Talata. Wanda shi ne kwana na goma sha uku a jere da ake samun kasa da 100.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG