Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Adadin Masu Kamuwa A Duniya Na Dada Karuwa


Wasu likitoci a Amurka lokacin da suke kokarin kawar da wata gawa

Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta bada rahoton hauhawar alkaluman sabbin kamuwa da cutar COVID-19 a fadin duniya da ya kai 183,000, adadi mafi yawa cikin wuni daya tun somawar annobar.

Jami’an WHO sun fadi cewa, cikin makonni da dama, an mai da hankali kan barkewar annobar a kasashen yankin Amurka kana, alkaluman da suka bayyana jiya lahadi sunyi nuni da hauhawar kididdigar sama da 116,000 a wuni guda a yankin.

Brazil ce take kan gaba da kusan sabbin kamuwa 55,000, Amurka ke biye da ita da sama da sabbin kamuwa dubu 36,000 kana Indiya na da sabbin kamuwa 15,000.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya

Shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus a yau Litinin ya ce, ba cutar ce ta kasance mafi girman barazana ba a yanzu, illar rashin hadin kai a fadin duniya da shugabanci.

Ya ce, “ba za mu iya shawo kan wannan annoba da rarrabuwar kai a duniya ba.”

Sama da jihohi 12 na Amurka ne su ke samun karuwar sabbin kamuwa da cutar. Dr. Tom Ingles, Darektan cibiyar lafiya a cibiyar nazarin lafiyar al’umma ta jami’ar Johns Hopkins a tattaunawarsa da kafar labaran Fox a jiya Lahadi, ya ce, dalilan wannan hauhawar shi ne samun karuwa gwajin cutar da ake yi da kuma kara yaduwar da take yi.

Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG