Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Afrika Za Ta Samu Karin Tallafi Daga WHO


Tambarin Hukumar lafiya ta WHO
Tambarin Hukumar lafiya ta WHO

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce za ta kara kudaden tallafin da take ba nahiyar Afirka don yakar cutar coronavirus.

Hakan na zuwa ne, yayin da ake samun karin mace-mace sanadiyyar cutar ta COVID-19 a nahiyar.

Duk da wannan yunkuri na WHO, yawan mace-macen da ake samu a nahiyar bai kai ko kusa da na sauran sassan duniya ba.

Amma Shugaban hukumar ta WHO, Tedros Ghebereyesus ya ce akwai alamu da ke nuna cewa alkaluma za su canza kan yadda cutar ta COVID-19 take ta’adi a nahiyar.

“Cikin makon da ya shude, an samu kashi 51 na karin adadin wadanda suka kamu da cutar a nahiyata, sannan an samu karin kashi 60 na wadanda suke mutuwa.”

Ya kara da cewa, “lura da matsalar karancin kayayyayin gwaje-gwaje da ake fuskanta, akwai alama da ke nuna cewa adadin zai fi haka.”

Rahotannin da aka ba WHO sun nuna cewa kusan mutum 19,000 aka tabbatar na dauke da cutar sannan kusan mutum 1,000 suka rasa rayukansu.

Hukumar kula da tattalin arziki ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa, cutar za ta kashe akalla mutum 300,000 kana za ta jefa wasu miliyan 30 cikin kangin talauci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG