Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Amnesty Ta Yi Gargadi Kan Cin Zarafin Jama’a


Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta tabbatar cewa jami’an tsaro basu ci zarafin mutane ba yayin da ake kokarin tabbatar da cewa kowa ya bi umarnin dokar zama a gida da aka kafa.

Kungiyar ta ce jami’an tsaro, ciki har da ‘yan sanda, dole ne su mutunta ‘yancin mutane yayin da suke kokarin tabbatar da cewa mutane sun zauna a gida.

Wannan dokar ta zama a gida na mako biyu dai shugaban kasar ta Najeriya, Muhammadu Buhari ne ya kafa ta a cikin makon da ya gabata domin takaita yaduwar cutar Coronavirus.

Wannan kiran na Amnesty na zuwa bayan da aka samu rahotanni masu cewa jami’an tsaro suna dukan fararen hulla wadanda suka keta wannan dokar.

Wani babban jami’i a kungiyar, Suen Bakari ya shaida wa Muryar Amurka cewa an samu karuwar cin zarafin mutane a kasar tun da aka kafa wannan dokar.

Ya ce “dole sai gwamnati ta tashi tsaye wajen tabbatar da cewa jami’an tsaro sun gudanar da aikinsu ba tare da tsangwamar jama’a ba.”

Dama dai an saba zargin ‘yan sanda a kasar da cin zarafin mutane ko kuma karbar na goro a hannunsu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG