Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: An Yi Kira Ga Duniya Ta Tuhumi China Kan Bacewar Dan Jarida.


Birnin Wuhan, inda cutar corona ta samo asali.
Birnin Wuhan, inda cutar corona ta samo asali.

Wani abokin Chen Qiushi, dan jaridar sa kai dinnan na China, wanda ya yi ta bayar da rahoto game da zanga-zangar rijin demokaradiyya da kuma bullar cutar COVID-19 kafin ya bace ranar 6 ga watan Fabrairu, ya yi kira ga duniya da kar ta mance da halin da wannan dan jaridar sa kai ya samu kansa ciki.

Chen dai ya yi ta bayar da rahotanni game da annobar daga Wuhan, ya na ta bayani ta bidiyoyin da ya yi ta sawa a kafafen youtube da twitter, wadanda kasar China ta hana hakan.

Abokin na Chen ya gaya ma Muryar Amurka cewa babu wanda ya san inda Chen ya ke. Abokin na Chen ya fadi ta kafar twitter cewa ta yiwu an yi wa dam jaridar da lauyansa daurin talala ne a gida.

“Yau kwanaki 86 kenan da ba a jin duriyar Chen Qiushi bayan da ya yi ta bayar da rahotanni game da coronavirus a Wuhan. Don Allah a cece shi!” Abin da abokin na Chen ya rubuta kenan ta shafinsa na kafar twitter ranar 3 ga watan Mayu, wato zagayowar ranar ‘yancin ‘yan jarida.

Sakon na tafe da hoton Chen da addu’a ga ‘yan jaridar sa kai da harshen Sinanci da cewa, “Sanin abu na sa a kasance da shiri, sanin abu na taimakawa wajen yanke shawara, sanin abu na barrantar da mutane.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG