Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Gwamnatin Ghana Na Jiran Sakamakon Gwaje-Gwajen Mutane 15,000


Kasar Ghana ta ce zata ci gaba da aiki da matakan dakile yaduwar cutar coronavirus (COVID-19) da ta riga ta dauka a kasar, yayin da ake jiran sakamakon gwaje-gwajen wasu mutane da aka killace.

Yanzu haka dai ana jiran sakamakon gwaje-gwaje na sama da mutane dubu goma sha biyar bayan da aka inganta shirin gwajin. Sakamakon shine zai tantance mataki na gaba da gwamnati zata bi.

Da yake jawabi ga al'ummar kasar akan matakan da suka dauka na dakile yaduwar cutar, Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo, ya ce sakamakon gwaje-gwajen shi zai ba gwamnati damar tsawaita dokar hana zirga-zirga ta makwanni biyu ko kuma a dakatar da ita.

Shugaban ya bayyana cewa a cikin matafiya dubu talatin da aka killace, biyar daga cikin su sun kamu da cutar, yayin da aka sallami mutane 800 daga cikin su, sannan ana shirin sallamar mutane 121 daga cikinsu.

Saurari karin bayani cikin sauti daga Ridwan Abbas.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG