Gwamnatin jihar Sokoto dake yankin arewa maso yammacin Najeriya, ta ce zata rufe iyakokinta daga karfe 12 na daren yau Juma’a 27 ga watan Maris, na tsawon makonni biyu don dakile bazuwar cutar coronavirus.
A wani taron manema labarai ne gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal ya shaida hakan. Ya kuma bayyana cewa matakan da aka dauka ba zasu shafi masu shigo da abinci da magunguna ba.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa an umurci ma’aikatan gwamnatin jihar daga mataki 12 zuwa kasa su zauna gida su rika gudanar da ayyukansu har tsawon makonni biyu. Sai dai gwamnan ya ce matakin bai shafi masu gudanar da ayyuka na musamman ba.
Wasu mazaunan jihar sun yaba da matakan da gwamnatin ta dauka, wasu kuma sun bukaci gwamnatin ta biya ma’aikata albashi kan kari don saukaka wa jama’a radadin yanayin da ake ciki.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton mutum 65 ne aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya, kuma babu mutum ko daya da aka samu da cutar a jihar Sokoto.
Ga Karin bayani cikin sauti daga Lamido Abubakar Sokoto.
Za ku iya son wannan ma
-
Maris 05, 2021
Fitaccen Dan Wasan Fina Finai Sadiq Daba Ya Rasu
-
Maris 04, 2021
A Nemi Taimakon Sojojin Haya Domin Yaki Da Boko Haram-Zulum