Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Ina Makomar Tattalin Arzikin Nahiyar Afirka?


Wata kasuwa a kasar Tanzania
Wata kasuwa a kasar Tanzania

Kwararru a fannin tattalin arziki na kira ga kasashen duniya da su kai wa nahiyar Afirka dauki saboda irin mummunan tasirin da ake fargabar annobar coronavirus za ta yi akan fannonin tattalin arziki da na kiwon lafiyar yankin.

Akwai dai kasashe a nahiyar da dama da ake kyautata zaton tattalin arzikinsu zai bunkasa cikin shekaru masu zuwa.

Sai dai masu fashin baki na fargabar cutar COVID-19 da take nuna jinkirin bayyana a nahiyar ka iya kassara ci gaban kasashen.

Hukumar da ke kula da fannin tattalin arziki a Majalisar Dinkin Duniya ta ECA, ta yi kiyasin cewa, tuni har nahiyar ta kashe dala biliyan 29 wajen yakar cutar ta coronavirus.

Kuma zai iya shafar kudaden shigarta musamman saboda yadda cutar ta dakile hadahadar saye da sayarwa a cewar hukumar.

“Akwai abubuwa da dama da ke da alaka da sauran asarar da za a yi, misali, takaita harkokin kasuwancin zai iya shafar kudaden da ke shiga lalitar gwamnati ya kuma rage kudaden da ke shiga hannun ‘yan kasuwa tare da dakile saka hannayen jari.” In ji Darektan hukuma ta ECA a gabashin Afirka Mama Keita yayin wata hira da aka yi da ita a CNBC Africa.

Baya ga haka, akwai kuma fargabar za a rasa ayyuka da dama, dalilin da ya sa masu lura da al'amuran yau da kullum suka ce akwai bukatar kasashen duniya su kai wa yankin dauki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG