Kasashen duniya na ci gaba da sassauta tsaurin matakan hana yaduwar cutar corona inkiya COVID-19.
Kasar Italiya ta fara sassauta matakan tsayar da yaduwar cutar ta corona daga jiya Litini, a yayin da karin jihohin Amurka ke ta sassauta tsaurin matakansu, don maido da hada-hadar tattalin arziki.
Italiyawa sama da miliyan hudu aka barsu su koma bakin aiki a jiya Litini, bayan killacewa mafi tsawon lokaci a Turai.
Ma’aikatan kamfanoni da na gine-gine sun fara ayyukansu, a yayin da aka kuma bar mutane su dan tattaka tare da ziyartar ‘yan’uwa.
Gidajen sayar da abinci sun yi ta cinikin kunshe-kunshen abinci a karo na farko tun bayan da aka fara hana zirga-zirgar.
Kasar ta tabbatar da adadin masu dauke da cutar ta corona wajen 212,000 da kuma wadanda cutar ta kashe wajen 29,000.
Jami’an kiwon lafiya sun ba da rahoton sabbin kamuwa da cutar wajen 195 jiya Litini, wanda ya yi sauki sosai idan aka kwatanta da sabbin harbuwa wajen 900 da aka yi ta samu kulluyaumin zuwa karshen watan Maris.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 18, 2021
Kungiyar Kasuwanci ta Duniya Na Bukatar Sabon Salon Gudanarwa-Dr. Ngozi
-
Fabrairu 18, 2021
Guterres Ya Yi Kiran a Samar Da Tsarin Bai Daya Na Rigakafin Coronavirus
-
Fabrairu 16, 2021
Kungiyar WTO Ta Gabatar Da Sabuwar Shugaba Ngozi Okonjo-Iweala
Facebook Forum