Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19 Na Bazuwa Kamar Wutar Daji a Najeriya 


Wata mata da aka yi wa gwaji a Najeriya
Wata mata da aka yi wa gwaji a Najeriya

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya ta ce adadin masu dauke da cutar coronavirus a kasar ya kara cillawa zuwa 1,273.

Hukumar ta NCDC, wacce ita ke da alhakin fitar da bayanan al’amuran da suka shafi cutar, ta ce an sake samun karin mutum 91 da ke dauke da ita a yinin jiya Lahadi.

Tun a makon da ya gabata ne dai adadin masu cutar yake hauhawa a kowace rana, inda a kullum yake kusantar 100 ko sama da haka.

Wannan adadi na mutum 1,273 dai an bayyana shi ne karfe 11:50 da daren 26 ga watan Afrilun shekarar 2020.

Ga jihohi 6 da suka fi yawan adadin wadanda cutar ta harba a Najeriya.

1 – Legas - 631

2 – Abuja - 141

3 – Kano - 77

4 – Ogun - 35

5 – Gombe - 35

6 - Osun - 34

Baya ga haka, mutum 239 sun samu warkewa daga cutar a Najeriyar, yayin da ta yi ajalin wasu 40.

Kara bazuwar da cutar ke yi a cikin Najeriya ya sa wasu jihohi na kara nazarin sabunta wa’adin kwanakin da suka kakkaba dokar hana zirga-zirga domin takaita yaduwar cutar.

Jihar Kaduna wacce cutar ta harbi mutum 15, ta kara saka dokar na tsawon kwannaki 30.

Gwamnan jihar Nasir El Rufai ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.

Ya kuma kara da cewa “za a ci tarar duk wanda ya karya wannan doka.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG