Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Najeriya Ta Haramta wa Matafiya Daga India, Brazil, Turkiyya Shiga Kasar


Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari

Najeriya ta dauki wannan mataki ne saboda yadda cutar coronavirus ke kara yaduwa a wadannan kasashe.

Hukumomin Najeriya sun ce daga ranar Talata, ba za a bari matafiya daga kasashen India, Brazil da Turkiyya su shiga kasar ba.

Najeriya ta dauki wannan mataki ne saboda yadda cutar coronavirus ke kara yaduwa a wadannan kasashe kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

Kwamitin yaki da annobar ta COVID-19 da shugaban kasa ya kafa ne ya sanar da wannan matsayin da kasar ta dauka a ranar Lahadi.

“Wadanda ba sa dauke da fasfo din Najeriya ko ba mazauna kasar ba, da suka ziyarci Brazil, India ko Turkiyya cikin kwana 14 gabanin zuwansu Najeriya, za a hana su shiga kasar,” wata sanarwa da Boss Mustapha ya fitar ta ce, wanda shi ne shugaban kwamitin yaki da cutar.

Likitoci akan wani mai fama da cutar COVID-19 a India
Likitoci akan wani mai fama da cutar COVID-19 a India

Matakin zai fara aiki ne daga ranar Talata 4 ga watan Mayu.

A ranar Asabar Najeriya ta bayyana samun sabbin mutum 43 da suka harbu da cutar, adadin da ya kai jimullar mutum dubu 165, 153 da cutar ta kama a kasar baki daya tun bayan barkewarta, kana ta kashe mutum 2,063.

Kamfanin dillacin labaran na Reuters ya ce, asibitoci, dakunan ajiye gawa duk sun cika makil yayin da India ta ba da rahoton samun sama da mutum dubu 300 da cutar ta harba a rana guda.

Kwana goma kenan a jere kasar ta India take samun wannan adadi a kullum.

Al’amura sun yi rincabewar da an bar iyalai da dama su nemi mafita da kansu.

Wani mara lafiya da ake tunanin yana dauke da cutar COVID-19 a Brazil (AP Photo/Eraldo Peres)
Wani mara lafiya da ake tunanin yana dauke da cutar COVID-19 a Brazil (AP Photo/Eraldo Peres)

A Brazil, duk da cewa adadin masu kamuwa da cutar ya ragu ba kamar yadda aka gani a karshen watan Maris ba, amma har yanzu, ana samun mutane da dama da cutar take harba.

Brazil ita ce ta biyu a duniya da aka fi samun wadanda suka mutu sanadiyyar cutar bayan Amurka.

Turkiyya kuwa ta saka dokar kulle a ranar Alhamis, wacce za ta kai har ranar 17 ga watan Mayu, a wani mataki na dakile yaduwar cutar da wadanda take kashewa.

Turkiyya ce kasa ta hudu a duniya da ta fi yawan wadanda cutar ta harba.

XS
SM
MD
LG