Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Shugaba Buhari Ya Yaba Da Gudummowar EU


shugaba Muhammadu Buhari

A yau Talata Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yaba wa kungiyar Tarayyar Turai da ake kira EU a takaice a game da gudummowar Euro miliyan 50, wato kimanin Naira biliyan 21 da ta ba Najeriya don tallafa wa kasar dakile yaduwar annobar cutar coronavirus.

A lokacin da yake marabtar tawagar kungiyar ta EU a Najeriya, wadda jakada Ketil Karlsen ya jagoranta, Shugaba Buhari ya ce wannan gudummowar zata taimaka sosai wajen tallafa wa kokarin da Najeriya ke yi wajen shawo kan cutar da kuma dakile yaduwarta a cikin al’umma, tare da farfado da tsarin kula da lafiya na kasar.

"Duk da cewa kungiyar EU na fuskantar babban kalubale a sakamakon wannan barkewar cutar, har yanzu tana da hangen nesa don tunawa da sauran kawayenta a duniya. Ina matukar farin ciki da godiya, a cewar Shugaba Buhari."

Shugaban ya kuma shaida wa wakilan EU cewa gwamnatinsa ta dauki matakai da yawa har zuwa yau a dangane da yaki da cutar COVID-19.

"Ya zuwa yanzu, adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya sun kai 343. Kokarinmu a matsayin Gwamnati, ya mayar da hankali ne akan dakile yaduwar cutar" a cewarsa.

Jakadan na EU ya jinjina wa Shugaba Buhari akan jawabin da ya yi wa ‘yan Najeriya a daren ranar Litinin, ya kuma jaddada cewa “lallai halin da ake ciki ba abun wasa ba ne kuma EU ta yaba masa saboda muhimman matakan da gwamnatinsa ta dauka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG