Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi wa kasashen da ke sassauta dokokin takaita zirga-zirga domin rage yaduwar coronavirus gargadi kan cewa idan ba su yi taka-tsantsan ba, za a koma gidan jiya.
A lokacin da shugaban ya ziyarci wani taro kan coronavirus da aka yi a birnin Geneva na kasar Switzerland ya ce, “Idan ba a sassauta wadannan dokokin a hankali ba, to tabbas wadannan kasashen za su dawo amfani da su daga baya.”
Tedros ya ce akwai matakan da kasashe ya kamata su bi kafin dage dokar tafiye-tafiye da kuma sauran dokokin da aka kafa domin takaita yaduwar wannan cutar.
Cikin matakan, ya kuma nuna bukatar samun wani tsari na sanya ido kan kowa, da kuma tabbatar da cewa fannin kiwon lafiya a kimtse yake.
Za ku iya son wannan ma
-
Mayu 26, 2023
An Yi Girgizar Kasa Mai Karfi A Gabashin Japan
-
Mayu 25, 2023
Tina Turner, ta rasu tana da shekara 83
-
Mayu 19, 2023
Babban Taron Kungiyar Kasashen Larabawa A Saudiyya
Facebook Forum