Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19 Ta Hana Taron Yakin Neman Zaben Trump a Florida


A jiya Alhamis shugaban Amurka Donald Trump ya sanar cewa ya soke babban taron jam’iyyar Repubican da za’a bashi tikitin takara da aka shirya gudanarwa a Jacksonville jihar Florida, a wata mai zuwa, sakamakon karuwar masu kamuwa da coronavirus. Duk da haka za a gudanar da ayyukan babban taron a jihar North Carolina.

Trump ya fada a Jacksonville cewa, “Yin babban taro bai dace a wannan lokaci ba.”

Shugaba Trump ya maida wani bangare na taron GOP zuwa Florida a watan da ya gabata bayan da suka samu sabani da shugabannin jam’iyar Democrat a jihar North Carolina kan gudanar da taron a rufaffen dakin taro tare da magoya bayansa ba tare da sun sa takunkumin rufe fuska ba.

Wasu wakilan jam’iyar Republican kalilan za su hallara a garin Charlotte na jihar North Carolina, don su zabi Trump a hukumance a ranar 24 ga watan Agusta. Trump ya ce zai yi jawabin amincewa a wani tsari na daban.

Trump wanda ya kwashe watanni yana nuna halin ko-in-kula game da tasirin annobar, inda a kwanan nan ma ya ce kashi 99 na yawan masu kamuwa da cutar da aka gani sun karu a Amurka, bai za zama da wata illa ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG