Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Trump Ya Ce a Bude Wuraren Ibada Bisa Wasu Sharuda


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka ya yi kira ga gwamnonin jahohi da su gaggauta sake bude wuraren ibada irinsu majami’u da haikalolin Yahudu da masallatai da duk sauran wuraren ibada, ya na mai kiransu mashahuran wurare da ke wasu muhimmancin harkoki a yayin da ake fama da annoba.

“Bisa umurni na, Cibiyar Hana Yaduwar Cututtuka za ta gabatar da ka’ida ga mabiya addinai .” a cewar Trump jiya Jumma’a.

Trump ya caccaki gwamnonin da “su ka dauki wuraren sayar da giya da na zubar da ciki a matsayin muhimmai amma banda majami’u da sauran wuraren ibada” a cewar Trump, ya na mai barazanar amfani da ikonsa na Shugaban kasa wajen jingine umurnin irin wadannan gwamnonin wadanda su ka cigaba da rufe wuraren ibada saboda dalilai na kariya.

McCain
McCain

Majami'ar Washington Cathedral

“Shugabannin majami’u, da pastoci, da shugabannin addinin Yahudu da shugabannin addinin Musulunci da dai sauran shugabannin addinai za su tabbatar da cewa masu zuwa ibada sun samu kariya a yayin da su ka taru don yin ibada,” a cewar Trump. Sharuddan da hukumar hana yaduwar cututtuka ta CDC ta gindaya sun hada da yadda za a rika tsaftace wuraren ibada da ruwan magunguna da kuma kwaskwarimar da za a yi a tsarin ibada.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG