Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: ‘Yan Banga Za Su Fara Tsare Iyakokin Gombe


Wasu 'Yan Banga a jihar Adamawa lokacin da suke samun horo daga 'yan sanda

Hukumomi a jihohin Bauchi da kuma Gombe sun gudanar da tarurruka na masu ruwa da tsaki kan batun neman inganta tsaro kan iyakokinsu bayan da aka samu karuwar masu dauke da cutar Coronavirus a jihohin.

Hakan na zuwa ne bayan da a Bauchi aka sake samun wani jami’in hukumar kula da lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya wanda ke dauke da cutar.

Hakan ya mayar da adadin ma’aikatan hukumar WHO masu cutar a Bauchi zuwa 2.

A jihar Gombe kuma gwamnan jihar ya ce za‘a shigar da maharba na gargajiya da kuma ‘yan banga domin sa ido akan iyakokin jihar dangane da masu shigowa jihar.

Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammed Kauran Bauchi ya bayyana a taron cewa “kasancewar cutar na ci gaba da yaduwa, mu ma dole mu kawo sabbin kudurori da za su taimaka wajen dakile cutar kamar ci gaba da kulle wurare a jihar nan.”

A jihar Gombe kuwa kwamishinan lafiya, Ahmed Gana, ya tabbatar cewa suna tsare da mutum biyar wadanda suka shiga jihar dauke da cutar Coronavirus.

“Yawancin wadanda suka shigo mana da cutar masu aikin acaba ne daga Legas,” a cewar kwamishinan.

Ya zuwa yanzu dai mutum 8 ne ke dauke da cutar a Gombe, yayin da Bauchi ke da mutum 5.

Saurari wannan rahoton a sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:22 0:00


Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG