WASHINGTON, DC —
Zakaran tamaular dan kasar Portugal ya shafe abin tarihin da Lionel Messi yayi na yawan kwallaye a raga a kakar gasar cin kofin zakarun kulob na Turai, a lokacin da ya zura kwallaye biyu a wasan da Real Madrid ta yi ta doke Bayern Munich da ci 4-0 jiya talata.
Kwallaye biyun da Ronaldo mai shekaru 29 ya jefa, ya kawo adadin kwallayensa a gasar ta bana zuwa 16.
A yanzu Ronaldo ya zarce kwallaye 14 da Messi dan kasar Argentina ya jefa cikin wasanni 11 na gasar ta shekarar 2011-12.
Wani abinda ya kara burgewa ma shi ne Ronaldo ya jefa wadannan kwallaye 16 ne cikin wasanni 10, domin bai buga wasan farko da Real Madrid ta buga da Galatasaray a zagayen farko ba.
Babu wani dan wasan da ya taba jefa kwallaye da yawa cikin dan kanakanin lokaci haka a wannan gasar cin kofin zakarun kulob na Turai, gasar da ita ce ta kwallon kafa mafi girma da tasiri a duk nahiyar Turai