Barkewar cutar Coronavirus a China ta shafi harkokin kasuwanci a wasu sassan duniya, ciki har da Najeriya.
Dubban 'yan kasuwar Najeriya su na zuwa China a kowacce shekara don shigo da kayayyaki. Amma hukumomin Najeriya sun yi kira ga 'yan kasuwa da su takaita zirga-zirga zuwa China har sai an magance cutar ta Coronavirus.
Najeriya da China manyan abokan huldar kasuwanci ne. A shekarar 2018, Najeriya ta shigo da kayayyaki na kimanin dala biliyan 7 daga China.
Masani a harkokin habbaka tattalin arziki Emeka Okengwu, ya ce, tasirin da cutar Coronavirus ke yi akan kasuwanci tsakanin Najeriya da China ana sa ran na wani dan lokaci ne.
Okengwu ya kara da cewa, lamarin zai iya yin tasiri kan kasuwanci saboda akwai wasu harkoki da za ka so a yi ido da ido wadanda ta yi wa hakan ba zai faru ba, musamman a wasu yankunan China. Amma lamarin ba zai dakatar da kasuwancin kasa da kasa ba. Ko shakka babu lamarin zai shafi wasu bangarorin kasuwancin, amma ba dorarren abu ba ne a cewar sa.