Kungiyar Agaji ta Red Kuros da Red Krisent ta kasa da kasa (IFRC, a takaice) ta ce barkewar annobar cutar Ebola da aka sake samu a Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo na kara munana, kuma har cutar ta kashe mutane sama da 1,000 zuwa yanzu.
Kungiyar ta IFRC ta fadi yau dinnan Asabar cewa cikin makon da ya gabata, an samu rahoton cewa mutane 23 ne kan kamu da cutar a duk rana, adadin da ba a taba gani ba tun bayan sake barkewar cutar a 2018.
Ma’aikatar Lafiya ta Janhuriyar ta Dimokaradiyyar Congo, jiya Jumma’a ta ce adadin wadanda su ka mutu ya karu zuwa 1,008.
Yawan tashe-tashen hankula ya dada kawo cikas a kokarin dakile sake barkewar cutar wanda kuma shi ne na biyu a mani a tarihin kasar, saboda a duk lokacin da aka samu dangarda a ayyukan jinya da kuma dakile yaduwar cutar, hakan kan janyo bazuwar cutar sosai.
Facebook Forum