Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Ebola Ta Kashe Mutane 43 A Congo


Ma'aikatan kiwon ladiya daga hukumar kiwon lafiya ta duniya da suke aiki a Congo domin kawar da cutar ebola
Ma'aikatan kiwon ladiya daga hukumar kiwon lafiya ta duniya da suke aiki a Congo domin kawar da cutar ebola

Gwamnatin Jamhuriyar Dimokradiyar Congo ta tabbatar da mutuwar mutane 43 tun daga lokacin da cutar ebola ta sake bulla a kasar

Gwamnatin jamhuriyar Congo tace bular anobar Ebola a gabashin kasar ta kashe mutane arba’in da tara tun farkon wannan wata, kuma kungiyar lafiya ta duniya tace ana fargaban samun karuwar wadanda suka kamu da cutar.

Karuwar yawan wadanda cutar ta kashe sannun kan hankali da kuma tsoron da ake ji cewa kimamin mutane dubu biyu sun kusanci wadanda suka kamu da cutar, ya dada cakuda al’amurran kasar, wadda tuni take fama da tarzoma da kuma rashin sanin tabbas akan makomar harkokin siyasa a kasar

A ranar daya ga watan nan na Agusta aka bada sanarwar bullar anobar a lardin Kivu ta arewa, a barkewar cutar ta baya bayan har ta kashe mutane arba’in da tara daga cikin mutane casa’in da aka bada rahoton sun kamu da cutar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG