Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Ebola Ta Shafi Lardi Na Biyu A Congo


Masu aikin kiwon lafiya dake kula da shawo kan cutar Ebola a Congo
Masu aikin kiwon lafiya dake kula da shawo kan cutar Ebola a Congo

Barkewar cutar ebola a kwana kwanan nan ya yadu har ya shafi lardi na biyu inda kawo yanzu mutane 30 suka kamu yayinda tuni 14 suka rasa rayukansu

Matsalar barkewar cutar Ebola ta baya-bayan nan a kasar Congo ta shafi wani lardi na biyu, a cewar ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da jami’an kiwon lafiya suka dukufa wajen gwajin makarin wannan cuta.

Jami’an na kiwon lafiya, na fatan yin amfani da magarin da ake kira mAb114, wanda ya samo asali daga wani da ya warke daga cutar ta Ebola a shekarar 1995, maganin da ake fatan zai yi tasiri a wannan karon na barkewar cutar.

Tuni dai an samu mutane 30 da ke dauke da cutar yayin da 14 daga cikinsu suka mutu.

Yanzu haka, kwararru na jiran a amince musu su fara amfani da wasu magunguna da dama a mataki na gwaji, a cewar ma’aikatar ta kiwon lafiya.

A makon da ya gabata, aka fara allurar rigakafin cutar ta Ebola a Maninga da Beni, manyan garuruwan da ke da tazarar tafiyar kilomita 30 daga cibiyoyin da aka samar na kula da wadanda suka kamu da cutar.

Yunkurin shawo kan wannan cuta ta Ebola, na fuskantar kalubalen kungiyoyi masu dauke da makamai a wannan yanki da ke kusa da kan iyakar Uganda, mai dauke da dumbin jama’a.

Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta yi kiran da a samar da hanyar da za a kai ga dukkanin jama’a da wannan cuta ta shafa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG