Wata fitacciyar ba-Iraniya ‘yar rajin kare hakkin mata, ta ce killace mutane da aka yi a kasar ya haddasa tashe tashen hankula tsakanin iyalai, wanda ya yi kama da abubuwan da aka yi ta gani a sauran sassan duniya.
A wata hira da Sashen Farsi na Muryar Amurka ranar Laraba ta wayar tarho daga arewacin Iran, Shahla Entesari ta ce wannan annobar ta haddasa munanan abubuwa ga iyalan Iraniyawa marasa karfi da kuma matalauta.
Rahoton Jami’ar Johns Hopkins game da cutar korona ya nuna cewar Iran na da masu dauke da cutar sama da 95,650 bisa ga alkaluman gwamnati, adadin da wasu kwararru a fannin lafiya ke zargin cewa ragewa gwamnatin Iran ta yi.
Facebook Forum