Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Kwalara Ta Sake Bayyana A Kudu Maso Yammacin Kamaru


Cholera
Cholera

Ana ci gaba da samun barkewar cutar kwalara a kasar Kamaru inda kungiyar agaji ta likitocin kasa da kasa da ake kira Médecin sans Frontières MSF ta gano mutum 189 sun kamu da ita a kudu maso yammacin kasar.

Kungiyar agaji ta likitocin kasa da kasa da ake kira Médecins Sans Frontières ko MSF ta aika da tawagar jami'an lafiya da magunguna domin daƙile yaɗuwar cutar ta kwalara a gundumomin Ekondo Titi, da Bakassi zuwa Mamfe, da ke yankin Kudu maso yammacin kasar Kamaru.

Ranar 27 ga watan Oktoban da ya gabata ne aka samu rahoton bullar cutar inda mutane aƙalla 189 suka harbu da ita yayin da bayanai ke cewa hakan ya faru ne sakamakon rashin tsarin kula da lafiya mai inganci, da kuma rikicin ‘yan awaren kasar da ya sa ake gani ta yiwu annobar ta dade ta na addabar al’ummar yankin fiye da yadda ake zato.

"Rikicin sashin renon Inglishi ya shafi matasa zuwa ƙabilu, a halin da ake ciki yanzu ana zaman fargaba, a cewar wata mazauniyar yankin. Ta kuma ce wasu lokutan akan ji harbe harben bindiga kuma ba fita da dare saboda yanayin da yankin ke ciki, shi ya sa a wannan lokacin ban iya kai dana asibiti ba dole na kira motar ɗaukar marasa lafiya.

Domin daƙile yaɗuwar cutar kungiyar MSF ta gaggauta tura tawagar ƙwararrun jami'anta don bada tallafi ga sauran jami’an kula da lafiya a waɗannan gundumomin. Duk da ƙalubale da rashin yarda da kungiyar ke fuskanta daga gwamnatin kasar hakan bai hana ta ayyukan ceton rayukan talakawa ba.

Wani mazauni a yanki ya fadi cewa wannan ne karo na biyu da ake gudanar da aiki a Edabato da ke Bakassi, wurawuren da aka ware don jinyar masu fama da kwalara.

Ko a shekarar 2019 sai da kungiyar likitocin ta MSF ta taimaka wajen daƙile yaɗuwar cutar kwalara a yankin Bakassi da ke Kudu maso yammacin Kamaru, inda aka yi wa mutane aƙalla dubu 39,000 allurar riga kafi.

Sai dai wannan karon jama'ar kasar na taka-tsan-tsan wajen karbar riga-kafin wanda su ke alakanta shi da na Coronavirus a cewar ɗaya daga cikin ma'aikatan lafiya a yankin, wanda ya ce sakamakon cutar COVID-19 jama'a na jan kafa kuma wannan ba shi ne karon farko da ake yin allurar riga kafi ba a Kamaru. An yi wa mutanen arewacin kasar riga kafi a shekarun baya kuma riga kafin na da tasiri.

Ƙasa da kashi 30 cikin 100 na al'ummar ƙasar na ƙin ziyartar asibitoci ko dai saboda jahilci ko kuma saboda sun fi son magungunan gargajiya na Afirka.

Ma’aikatan lafiya na kira ga farar hula da su gaggauta mika waɗanda ake zargi da kamuwa da cutar kwalara zuwa asibitoci mafi kusa.

Saurari cikakken rahoton Mohamed Bachir Ladan:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

XS
SM
MD
LG